WANENE ANNABI ISA ALMASIHU
Daga Saminu Kadaura.
Isa Almasihu ya taba yin wannan tambaya wa almajiransa, “Wa mutane suke cewa Nake?” (luk.9:18). Wannan fa ya kasance babban tambaya mai muhimminci da ke fuskantar dan Adam. Har zuwa karshen zamani annabi Isa Almasihu zai zama sanadin rarrabuwar kawuna sakanin kungiyoyi, al’adu da masana. Kiristoci duk duniya a shekaru masu yawa da suka gabata har wa yau sun bada gaskiya cewa a cikin Isa Almasihu kadai ake samun ainihin sulhu sakanin mutum da Allah.
Za mu iya yin wannan tambaya cewa, “Mai ya sa Kiristoci suka bada gaskiya ga Allahntakar Isa Almasihu?” Za a sami ansar cikin wadannan shaida na Allantakar Yesu Almasihu kamar haka:
1. Kimanin sawon shekaru dubu daya an rubuto anabce anabce da suka yi anabcin zuwan Almasihu daga sama, wadda shine zai zama mai ceton duniya. Shi daga zuriyar Ibrahim, daga kabilar Yahuza, daga kuma iyalin Dauda, zai zama mai girma, Allah madawami. Shekaru masu yawa kafin haihuwar Isa Almasihu an san da wadannan anabce-anabce an kuma karbe su.
2. Annabi Isa Almasihu ne kadai a cikin dukan annabawa na da rai madawami. Shine kadai da ya kasance jiya, yana raye a yau da kuma gobe da har abada (Yah.1:15; Ibra.1:1-3).
3. Annabi Isa Almasihu ne kadai cikin dukan annabawa da aka dauki cikinsa daga Ruhu Mai Tsarki aka haife shi ta wurin budurwa Maryamu (Ish.7:14; Mat.1:18-23)
4. Isa Almasihu ne kadai a cikin dukan annabawa da Allah Uba ya ce, “wannan shi ne Dana kaunataccena, wanda nake farin ciki da shi kwarai” (Mat.3:7). Isa Almasihu ya kuma ce; Da Ni da Ubana daya ne” (Yah.10:30)
5. Lokacin da Annabi Isa Almasihu ke a duniya ya tayar da matattu zuwa rai, kamar da aka nuna cikin ayoyin nan na linjila, “Ya kusaci kofar garin ke nan, sai ga wani mamaci ana dauke da shi, shi kadai ne wajen uwa tasa, mijinta kuwa ya mutu. Mutanen gari da yawa sun rako ta. Da Ubangiji ya gan ta, ya ji tausayinta, ya kuma ce mata, “Daina kuka” Sa’an nan ya matso, ya taba makarar, masu dauka kuma suka tsaya cik. Sai Yesu ya ce, “Samari, na ce maka ka tashi.” Mamacin ya tashi zaune, ya fara Magana. Yesu kuwa ya ba da shi ga uwa tasa” (Luk.7:12-15).
6. Annabi Isa Almasihu ne kadai a cikin dukan annabawa, ya kasance da siffa ko kamannin dan Adam da ta surar Allah a game baki daya cikin rayuwarsa a nan duniya; mutum ne ainihin sahihi, Allah ne kuma ainihin gaskiyar (Filb.2:5-9).
7. Duka annabawa sun yi zunubi, amma annabi Isa Almasihu shi kadai ya kasance sahihin gaskiya mai tsarki, babu zunubi ko kadan a rayuwarsa (Yah.8:46; 1Bitr.2:22).
8. Annabi Isa Almasihu ne kadai a cikin dukan annabawa, shine hasken daukakar Allah, ainihin kamanin zatinsa kuma, Shi ne surar Allah marar ganuwa,” A gare shi dukan cikar Allah ta tabbata domin Allah na farin ciki da haka (Ibra.1:3; Kol.1:15; Kol2:9)
9. Annabi Isa Almasihu ne kadai a cikin dukan annabawa, ya sha azaba. Ya mutu bisa giciye domin zunubanmu, an binne shi amma a rana ta uku, ya tashi daga matattu sabo da fansar mu daga zunubi, ya kuma ba da yanci da rai madawami ga duk wanda ya bada gaskiya gare shi (Ayuk. Man.4:12)
10. Isa Almasihu ne kadai a cikin dukan annabawa babu farko da karshe, Ya mutu amma gashi yanzu, shi rayayye ne har abada abadin. Yana kuwa da mabudan mutuwa da na Hades (Wah. Yah.1: 18). Almasihu ne kadai ke da iko ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato Iblis, ta mutuwarsa ya kuma yantar da duk wadanda tun haifuwarsu suke zaman bauta saboda tsoron mutuwa (Ibr.2:14)
▪▪Don karin bayani ko tambaya ka tuntubi Saminu Kadaura (08034152198). Malam Kadaura yana zama cikin Asaba a jihar Delta